Martanin Siriya kan firicin Ministan harakokin wajen Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1486-martanin_siriya_kan_firicin_ministan_harakokin_wajen_saudiya
Ma'aikatar Harakokin wajen Siriya ta mayar da martani kan faricin da Ministan harakokin wajen Saudiya ya yi na canza Gwamnatin kasar
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Feb 29, 2016 13:38 UTC
  • Martanin Siriya kan firicin Ministan harakokin wajen Saudiya

Ma'aikatar Harakokin wajen Siriya ta mayar da martani kan faricin da Ministan harakokin wajen Saudiya ya yi na canza Gwamnatin kasar

Tashar Telbijin din Almanar ta kasar Lobnon ta habarta cewa a yau Litinin Ma'aikatar harakokin wajen kasar Siriya ta mayar da martanin dangane da firicin ministan harakokin wajen Saudiya Adil Jubair na cewa dole ne duniya ta gabatar da wani tsari wanda zai maye gurbin gwamnatin kasar Siriya, a cewar Ma'aikatar harakokin wajen Siriyan wannan wani mafalkine da magabatan saudiyan ke yi da kuma ba zai tabbatu ba.

Ma'aikatar harakokin wajen Siriyan ta tabbatar da cewa firicin na Adil Jubair shiri ne na magabatan HKI da Amurka, kuma hakan shike tabbatar da cewa magabatan saudiya na zartar da shirin Amurka da Haramcecciyar kasar Isra'ila.

A yayin da yake bayyani kan halin da gabas ta tsakiya ke ciki, a daren jiya Lahadi , Ministan harakokin wajen Saudiya Adil Jubair ya sake nanata cewa wajibi ne shugaban kasar Siriya Bashar Al-asad ya sauka daga kan karagar milki, kuma yana zabi guda biyu ko ya sauka cikin ruwan sanhi ko kuma a kifar da shi da karfin Soja.