Syria: An gano kamfanin kera makamai A Gabacin Aleppo
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i14962-syria_an_gano_kamfanin_kera_makamai_a_gabacin_aleppo
Sojojin Syria Sun gano Kamfanin Kera Makamai
(last modified 2018-08-22T06:59:21+00:00 )
Dec 07, 2016 08:29 UTC
  • Syria: An gano kamfanin kera makamai A Gabacin Aleppo

Sojojin Syria Sun gano Kamfanin Kera Makamai

Sojojin gwamnatin Syria sun gano  wani kamfanin kera makamai na 'yan ta'adda a gabacin birnin Aleppo da su ke fafatawa da su.

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ce; kamfanin da sojojin su ka gano wanda ya ke a unguwar Hanano, ana kera makamai masu guba da kuma roka-roka a cikinsa.

Makwanni biyu da su ke gabata ne dai sojojin na Syria su ka sanar da kame unguwar Hanano daga hannun 'yan ta'adda.

Kawo ya zuwa yanzu dai sojojin na Syria suna samun nasara akan 'yan ta'adda, kuma gabacin birnin na Aleppo na gab da shiga hannun sojojin gwamnati da kawayensu.