Sojojin Gwamnatin Iraki Sun Halaka 'Yan Kungiyar Da'ish Fiye Da 60
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1501-sojojin_gwamnatin_iraki_sun_halaka_'yan_kungiyar_da'ish_fiye_da_60
Sojojin gwamnatin Iraki sun halaka 'yan ta'addan kungiyar Da'ish fiye da 60 a yankuna daban daban da suke lardin Anbar da ke yammacin kasar Iraki.
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Mar 01, 2016 01:40 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Iraki Sun Halaka 'Yan Kungiyar Da'ish Fiye Da 60

Sojojin gwamnatin Iraki sun halaka 'yan ta'addan kungiyar Da'ish fiye da 60 a yankuna daban daban da suke lardin Anbar da ke yammacin kasar Iraki.

Kwamandan lardin Anbar da ke yammacin kasar Iraki Isma'il Mahlawi ya sanar da cewa; A samamen da sojojin gwamnatin Iraki suka gudanar da yankuna daban daban da suke lardin Anbar musamman a yankin Ha'midiyya, Bouziyab, Bouda'iyj da yankin Salam sun yi nasarar kashe 'yan ta'addan kungiyar Da'ish 64.

Har ila yau sojojin gwamnatin Iraki sun samu nasarar lalata bama-bamai fiye da 100 a yankunan da suka gudanar da samamen a jiya Litinin. Kamar yadda sojojin na Iraki suna samu nasarar tarwatsa rumbun tsimin man fetur da 'yan ta'addan kungiyar Da'ish suke amfani da shi a garin Ramadi da ke lardin na Anbar.