Kasar Masar Ta Shimfida Sharuddan Sake Hulda Da Kungiyar Hamas
Gwamnatin kasar Masar ta bukaci kungiyar Hamas ta Palasdinawa ta cika sharudda guda ukku kafin ta amince da maida hulda tsakaninta da ita kungiyar.
Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto wani jami'in kungiyar ta Hamas wanda bai so a bayyana sunannsa ba yana cewa sharuddan da gwamnatin kasar Masar ta shimfida wa kungiyar sun hada da tabbatar da tsaron kan iyakar kasashen biyu mai tsawon kilomita 14 da ke kudancin yankin Gaza, hana yan ta'adda masu tsatsauran ra'ayin addinin daga yankin na Gaza shiga yankin Sina na kasar ta Masar da kuma hana masu laifi daga kasar Masar wadanda suke shiga yankin Gaza don kubuta daga hannun kotunan kasar.
Kungiyar ta Hamsa dai ta musanta zargin cewa akwai masu laifuffuka yan kasar Masar da suke shigar yankin na Gaza don gujewa mahukantan kasar ta Masar, sannan suke kuma samun goyon bayan kungiyar.
Dangantakar kasar Masar da kungiyar Hamasa ta yi tsami ne tu bayan kafar da gwamnatin Muhammad Mursi a cikin watan Yulin shekara 2013.