Irak : Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 11
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16276-irak_harin_kunar_bakin_wake_ya_kashe_mutane_11
Rahotonni daga Iraki na cewa mutane akalla 11 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a birnin Bagadaza.
(last modified 2018-08-22T11:29:30+00:00 )
Jan 08, 2017 11:56 UTC
  • Irak : Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 11

Rahotonni daga Iraki na cewa mutane akalla 11 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a birnin Bagadaza.

Bayanai sun nuna cewa dan kunar bakin waken ya kai harin ne da mota a safiyar wannan Lahadin a harabar kasuwar kayan lambu dake birnin kamar yadda kakakin ma'aikatar cikin gida na kasar, Saad Maan ya tabbatar.

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu 35 da suka raunana kamar yadda wata majiyar asibiti ta shaidawa kanfanin dillancin labaren AFP.

Har kawo lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, saidai so tarin yawa  akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'addin ga kungiyar nan ta IS.