Karshen Taron Astana Kan Rikicin Syria
Kasashen Iran, Rasha da Turkiyya sun jadadda goyan bayan su akan shirin samar da zaman lafiya ta hanyar siyasa a kasar Syria.
Kasashen dai sun bayyana hakan ne a sanarwa karshen taron su na kwanaki biyu daya gudana a birnin Astana na kasar Kazakhstan, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin kasar Syria.
Wannan taron dai na daga cikin matakan da kasashen suka dauka a yayin wani taron ministocin harkokin wajensu na watan Disamba bara a birnin Moscow daya samu goyan bayan kwamitin tsaro na MDD domin farfado da tattaunawar zamen lafiya tsakanin gwamanti da 'yan tawaye na kasar Syria.
A sanarwar da suka fitar yau a karshen taron kasashen da suka hada da Iran, Turkiyya da Rasha sunce suna goyan bayan tattaunawar masu rikici a kasar ta Syria.
kana suna jinjinawa wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar Syria wanda halartar shi a taron na Astana ta taimakawa tattaunawar matuka.
A wani share kuma kasashen sun kara jadada goyan bayan su na ganin Syria ta ci gaba da zama intacciyyar kasa mai cike da mulki, 'yancin kai, hadin kai da yankunanta bisa tsarin demokuradiyya data kunshi kabilu daban daban inda kuma kowa yake da 'yancin ya rungumi akidarsa.