Fira Ministan Iraki Ya Mai Da Martani Kan Furucin Shugaban Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16987-fira_ministan_iraki_ya_mai_da_martani_kan_furucin_shugaban_amurka
Fira ministan Iraki ya jaddada cewa: Mai fetur da ke Iraki mallakin al'ummar kasar ne, don haka babu wata kasa da take da hurumin juya alakar sarrafa dukiyar man fetur ta kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 25, 2017 07:09 UTC
  • Fira Ministan Iraki Ya Mai Da Martani Kan Furucin Shugaban Amurka

Fira ministan Iraki ya jaddada cewa: Mai fetur da ke Iraki mallakin al'ummar kasar ne, don haka babu wata kasa da take da hurumin juya alakar sarrafa dukiyar man fetur ta kasar.

A taron manema labarai da ya gudanar a jiya Talata: Fira ministan Iraki Haidar Abadi ya bayyana cewa: Furucin shugaban kasar Amurka Donald Trump na cewa: Amurka zata yi amfani da kudaden man fetur na kasar Iraki wajen biyan kudaden da ta kashe a lokacin yakin da ta kaddamar kan kasar ta Iraki a shekara ta 2003 da ya kawo karshen mulkin kama karyar gwamnatin Saddam Husain, furuci ne da ke bukatar karin haske, amma a fili yake cewar dukiyar man fetur ta Iraki mallakin al'ummar kasar ne zalla.

Haidar Ibadi ya kara da cewa: Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya aike da wasika ga mahukantan Iraki da a ciki yake bayyana shirin sabuwar gwamnatinsa na kara yawan taimakon da take bai wa kasar ta Iraki musamman a fagen yaki da ta'addanci.