Gwamnatin Lebanon Ta Kame Mutane 5 Suna Leken Asiri Ga HKI
Gwamnatin kasar Kebanon ta kama mutane hudu a kasar sunawa HKi aikin Leken asari.
Bangaren yada Labarai na ma'aikatar Tsaron kasar ta Lebanon ce ta bayyana haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa mutanen sun tabbatar mata kan cewa ta mika bayanai da dama ga HKi ta hanyar ofisoshin jakadancinta a kasashen Turkia, Jordan, Britani da kuma Nepal.
Bayanin da ma'aikatar tsaron kasar ta Lebanon ta ce biyu daga cikin wadanda aka kama yan kasar ta Lebanon ne wadanda aka haifa a shekaru 1977 da 1982. Sai kuma dan kasar Palasdinu guda wanda aka haifa a shekara ta 1992. Sannan akwai yan kasar Nepal guda biyu mata wadanda aka haifa a shekaru 1991 da 1993.
Rahoton ya kara da cewa ma'aikatar tsaron ta sami wannan nasara ce bayab bin duddugin wadan nan mutane na lokaci mai tsawo kafin dubunsu ta cika.
Daga karshe rahoton ya kammala da cewa a halin yanzu a mikasu ga wata kotu a kasar ta Lebanon don fuskantar sharia a kan laifuffukan da ake tuhumarsu da su.