Taron Kasashen Iran, Rasha Da Turkiyya Kan Batun Syria A Astana
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17377-taron_kasashen_iran_rasha_da_turkiyya_kan_batun_syria_a_astana
Yau Litinin wakilan kasashen Rasha, Iran, da Turkiyya na taron su zagaye na biyu a birnin Astana domin tattauna yadda za'a samar zamen lafiya a kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 06, 2017 07:39 UTC
  • Taron Kasashen Iran, Rasha Da Turkiyya Kan Batun Syria A Astana

Yau Litinin wakilan kasashen Rasha, Iran, da Turkiyya na taron su zagaye na biyu a birnin Astana domin tattauna yadda za'a samar zamen lafiya a kasar Syria.

Taron wanda ya hada kwararu na kuma samun halartar wakilin MDD dana kasar Jordan domin tattauna yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta mai daurewa a  da kuma bukatar da 'yan tawayen na Syria suka gabatar a wacen taron.

Wannan dai ita ce haduwa ta biyu ta tsakanin kasashen Rasha, Iran da Turkiyya kan rikicin kasar ta Syria a Astana, bayan wace sukayi a ranakun 23 da 24 na watan Janairu daya gabata.

A wacen taron da suka gudanar bangarorin sun cimma matsaya kan batun fitar da 'yan adawa masu daukeda makamai da kuma gungun 'yan ta'adda a gabashin birnin Halep da kuma tsagaita wuta na dukkan bangarori a kasar ta Syria da rikicin shekaru shida ya daidaita.