Kalubalen Da Tattaunawar Gwamnati da 'Yan Adawan Siriya Ke Fuskanta
Shirye-shiryen tattaunawar ta wannan Litinin na fuskantar kalubale da ya hada da rashin cimma daidaito tsakanin 'yan adawa kasar Siriya akan wadanda zasu wakilce su.
A wannan Litinin ce aka tsara gudanar da tattaunawar da zata hada wakilan gwamnati dana 'yan adawa Syria domin kawo karshen yakin daya ki ci yaki cinyewa a kasar ta Syria
saidai a halin yanzu babban kalubalen da tattaunawar ke cin karo da ita, shi ne na rashin samun daidaito tsakanin 'yan adawa kasar da suka fahimtar juna akan wadanda zasu wakilce su a tattaunar, lamarin da a cewar wasu majiyoyi tuni akayi hasashen gusa tattaunar da 'yan kwanaki .
kafin hakan kuma babban mai shiga tsakani na bangaren 'yan adawan Syria Mohammed Alloush ya kalubalanci matsin lamba da Amurka keyi musu na su gaggauta shiga tattaunar.
Tuni dai Gwamnatin Siriya ta mikawa MDD jerin sunayen wakilan ta a tattaunawar da za'ayi ta Geneva .
ministan harkokin wajen Siriya ne Fayçal Moqdad zai jagoranci tawagar tareda wakilin kasar a MDD Bashar Jaafari, akwai kuma wasu jami'an diflomatsiya uku dama wasu lauyoyi takwas.
wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da har yanzu 'yan adawa kasar basu kai ga fahimci juna ba akan wadanda zasu wakilce su a tattaunawar, lamarin da zai iya kawo jinkiri a tattaunawar da ake sa ran somawa a wannan Litinin 25 ga watan January nan da muke ciki.
a jadawalin da MDD ta gabatar ana bukatar tsagaita, kafa gwamnatin wucin gadi cikin watanni shida da kuma gudanar da zaben gama-gari cikin watanni 18.
A halin da ake ciki dai sojojin gwamnatin kasar Syria na ci gaba da samun galaba a fafatawar da suke yi da 'yan tawayen kasar musamen a jihar Lattakia dake arewacin kasar inda suka yi nasarar kwato garin Rabia, muhimmin sansanin dakaru masu adawa na kasar.
Wani jami'in bangaren soja na kasar Syria ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kwato garin Rabia dake da nisan kilomita 60 daga arewa maso gabashin birnin Lattakia ne sakamakon taimakon sojojin fararen hula da ke wurin.
Shi dai wannan wuri yana dab da kan iyakar Syria da Turkiya ne. Sojojin injiniyoyi na gwamnatin kasar suna gudanar da aikin kawar da boma-boman da dakarun masu adawa suka binne a garin.
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, garin Rabia yana daya daga cikin manyan sansanonin dakarun masu adawa dake jihar Lattakia.
A 'yan makwannin da suka gabata, sojojin gwamnatin kasar Syria sun samu babban ci gaba a yankin arewacin jihar Lattakia, inda suka kwato garuruwa da dama. Bayanai na cewa, sojojin gwamnatin kasar za su ci gaba da dannawa zuwa kan iyakar kasar da ke gabashin jihar Lattakia da jihar Idlib.