Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Kauyuka A Kudancin Al-Bab
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17501-sojojin_siriya_sun_kwato_wasu_kauyuka_a_kudancin_al_bab
Sojojin Siriya sun sami nasarar kara tabbatar da ikonsu a lardin Halab (Aleppo) mai matukar muhimmanci bayan da suka sami nasarar kwace wasu garuruwa da kauyuka bayan gagarumin gumurzu tsakaninsu da 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS).
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 10, 2017 02:03 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Kauyuka A Kudancin Al-Bab

Sojojin Siriya sun sami nasarar kara tabbatar da ikonsu a lardin Halab (Aleppo) mai matukar muhimmanci bayan da suka sami nasarar kwace wasu garuruwa da kauyuka bayan gagarumin gumurzu tsakaninsu da 'yan ta'addan kungiyar Da'esh (ISIS).

Kafafen watsa labaran kasar Siriyan sun bayyana cewa sojojin Siriyan sun sami nasarar kwato kauyuka da dama da suka hada da Touman, Uwaishiyah and Hawarat Tadef da suke kudancin garin al-Bab da ke hannun 'yan ta'addan na Da'esh inda a halin yanzu suke ci gaba da tsarkake garuruwan daga bama-bamai da nakiyoyin da 'yan ta'addan suka dasa kafin gudun su daga garin.

Har ila yau kuma sojojin kasa na Siriyan da suke samun goyon bayan sojojin sama sun kai wasu hare-hare kan sansanonin 'yan Da'esh din da ke garin Dayr al-Zawr da ke gabashin kasar inda suka kashe wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan da kuma tarwatsa makamansu.

Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Siriyan suke ci gaba da samun nasararori a kan 'yan ta'addan na Da'esh da sauransu a sauran yankuna na kasar.