Syria : An Sake Gayyatar Bangarorin Dake Rikici Kan Tebirin Tattaunawa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Kazakstan ta ce an sake gayyatar bangaren gwamnati da 'yan tawayen Syria a wani sabon zagayen tattaunawa sulhu da za'ayi a tsakiyar watan Fabrairu nan a birnin Astana.
Sanarwar ta ce za'a sake gudanar da wani taro na babban matsayi a birnin Astana a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Fabrairu nan a ci gaba da zamen tattaunawar Astana domin samar da zamen lafiya tsakanin bangarorin dake rikici a Syria.
An dai gayyaci bangaren gwamnati da 'yan tawayen na Syria masu daukeda makamai da kuma wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar ta Syria Staffan de Mistura a wannan zagayen tattaunawa ta shiga tsakanin kasashen Rasha, Turkiyya da kuma Iran.
Ko baya ga hakan an gayyaci tawagar kasashen Jodan da kuma Amurka a mastayin masu sa ido a tattaunawar mai zuwa.
Tattaunawar dai zata fi maida hankali kan yadda za'a mutunta yarjejeniyar tsagaita da aka cimma da kuma yadda za'a daidaita wasu al'amura a wasu jihohin kasar ta Syria.