Shuwagabannin Kasar Libya Sun Kasa Haduwa Da Juna A Kasar Masar
Wata majiya a kasar Masar ta bayyanawa muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran kan cewa Priministan gwamnatin hadin kan kasar Libya da kuma Janar Khalifa Hatfar shugaban rundunar jojin kasar mai mazauni a Bengazi sun kasa haduwa da juna a birnin Alkahira dun da cewa suna cikin birnin.
Khalifa Haftar shugaban sojojin kasar Libya wanda ke iko da yankin gabacin kasar ya ki yarda ya yi ido hudu da Fa'iaz suraj don tattauna batun yerjejeniyar Sukhairat ta hada kan kasar a birnin Alkahira.
Shuwagabannin biyu duk sun isa birnin Alkahira a ranar Litinin, amma Khalifa Haftar ya gana da Mahmood Hijaji babban hafsan hafsoshin sojojin kasar masar wanda gwamnatin kasar ta Masar ta dorawa nauyin kula da matsalar kasar ta Libya, inda bangarorin biyu suka tattauna batun matsalolin kasar ta Libya.
Labarin ya kara da cewa Priministan gwamnatin hadin kan kasar ta Libya Fa'iz Suraj ya koma gida a safiyar yau Laraba bayan bayan ya tabbatar da cewa ganawa da Khalifa haftar ba zai yu ba.
Banda haka bangarorin yan siyada ta kasar Libya daban daban suna ci gaba da tattauna matsalolin kasar a birnin na Alkahira.