Hizbullah Ta Bukaci HKI Ta Rufe Cibiyar Makaman Nukliarta Ta Dimono
Shugaban kungiyar Hizbullah ta Kasar Lebanon Sayyeed Hassan Nasarallah ya bukaci HKI ta ta gaggauta rufe cibiyan makaman nuclear ta ta Dimona.
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyeed Nasaralla yana fadar haka a jiya Alhamis a lokacinda yake jawabin kan zagayowan ranar tunawa da shaheedan kungiyar da kuma ranar sojojin sojojin kasa.
Sayyeed Nasarallah ya kara da cewa a baya dai HKI ta amince da gargadin kungiyar na san cewa tana iya fasa tanakunan iskar gas mai guba ta Ammonia mallakinta a inda ta ijiyesu. Sai ta boye su a wasu wurare. ko ina suke dai zamu kai garesu. Amma a wannan karon muna gargadin ta da ta wargaza cibiyar makaman nukliyarta ta Dinoma don ita ma tana daga cikin wurtaren da makamammu zasu iya kaiwa a duk wani takalat fada da zata yi.
Dangane da sabon shugaban kasar amurka kuma Sayyeed Nasarallah ya ce har yanzu ba'a san inda ya sa gaba, don matsalolin da yake fuskanta a cikin majalisar gudanarsa har yanzu sun isheshi.