Dakarun Iraki sun bukaci Al'ummar Mausil da su fice daga birnin
Cikin wata sanarwa da suka watsa Dakarun Saman Iraki sun bukaci Al'ummar Mausil da su fice daga cikin Birnin domin tsarkake shi daga 'yan ta'addar ISIS
A wani sako da suka raba ga milyoyin Al'ummar yankin yammacin Mausil, Dakarun saman Iraki sun bayyana cewa za su kaddamar da hare-hare domin 'yanto garin daga kangin mayakan 'yan ta'adda na ISIS.
Tun a jiya Assabar, Ma’aikatar tsaron kasar ta ce jiragen yakin sama na ta watsa wasu takardu da ke gargadin mazauna yammacin birnin Mosul su kauracewa gwabzawar da za a yi da mayakan IS.
Rahotanni sun ce tuni dakarun gwamnati suka yiwa mayakan kawanya a garin, inda aka kiyasta akwai fararen hula sama da dubu 650.
Takardun da aka raba sun ce tuni dakarun gwamnati suka fara danna kai cikin birnin na Mosul domin fatattakar mayakan na IS.