Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Ya Ziyarci Iraki, Karon Farko Tun 2003
Ministan harkokin wajen Saudiyya, Adel al-Jubeir, ya fara wata ziyara aiki a kasar Iraki inda ya gana da mahukuntan kasar a wani yunkuri na farfado da alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Wannan dai ita ce ziyara wani ministan harkokin wajen Saudiyya ta farko a Iraki tun bayan shekara 2003.
Wata sanarwa da offishin fira ministan kasar Iraki ya fitar ta ce Bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi hulda tsakanin kasashen biyu ciki hada batun yaki da kungiyar 'yan ta'addan Da'esh.
Wannan ziyara dai na zuwa ne a daidai lokacin da dakaruin kasar Iraki ke ci gaba da fatatakar 'yan ta'addan na IS a yankin Mosul dake zamen sansaninsu na karshe a Iraki.
Haka kuma a yayin ziayara tasa Ministan harkokin wajen na Saudiya ya gana da takwaransa na Iraki Ibrahim al-Jaafari wanda a cen baya ya sha sukan mahukuntan Saudiyya akan abunda ya kira shishigi a cikinharkokin kasar ta Iraki.
Kasashen Iraki da Saudiyya dai nada sabani akan mayakan sa kai 'yan shi'a dake yaki da kungiyar 'yan ta'addan Da'esh.