Gwamantin Syria Za Ta Maida Martani Kan Harin Homs
Gwamanatin Syria ta sha alwashin maida martani mai tsanani kan harin da tsohuwar kungiyar reshen Al'Qaida ta kai a birnin Homs wanda ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 40.
Da yake bayyana hakan ga manema labarai, wakilin tawagar gwamnati Syria a tattaunawar dake gudana yanzu haka a Geneva kan rikicin kasar ta Syria, ya ce harin da 'yan ta'ddan suka kai a Homs ba abun da za'a taba rufe ido akansa ba, don haka gwamnatin kasar za ta maida martani mai tsanani.
Mista Bachar al-Jaafari ya fadwa manema labarai cewa sun lura a duk lokacin da ake wata tattaunawar neman zamen lafiya sai an samu wasu masu bakar anniya da zasuyi duk wani yjunkuri na maida hannun ogogo baya.
Dama kafin hakan shi ma wakilin MDD kan rikicin kasar ta Syria Stafan De Mistura ya yi irin wadanan kalamen na cewa harin na Homs na nemen cutura da tattaunawar da ake ne a Geneva da nifin samar da zamen lafiya a Syria.
Harin dai da tsohon reshen kungiyar Al'Qaida a Syria ya kai a kan cibiyar leken asiri ta Homs ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 40 ciki har da shugaban cibiyar leken asisrin ta Homs, Hassan Daaboul, wanda wani na kusa da shugaba Basharul Assad, wanda kuma sannane ne a hukumar leken asiri ta Syria.