Jiragen Amurka Sun Safke Wa ISIS Wasu Akwatuna A Mausul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18046-jiragen_amurka_sun_safke_wa_isis_wasu_akwatuna_a_mausul
Jiragen sojin Amurka sun safke wasu akwatuna da ake sa ran suna dauke ne makamai a yankin Talafar da ke yammacin Mausul da ke karkashin ikon 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS.
(last modified 2018-08-22T06:59:44+00:00 )
Feb 26, 2017 08:47 UTC
  • Jiragen Amurka Sun Safke Wa ISIS Wasu Akwatuna A Mausul

Jiragen sojin Amurka sun safke wasu akwatuna da ake sa ran suna dauke ne makamai a yankin Talafar da ke yammacin Mausul da ke karkashin ikon 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS.

Dakarun sa kai da ke yaki tare da rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci a Iraki ta sanar da cewa, ta hango jiragen sojin Amurka suna safke wasu akwatuna a yankin yammacin Mausul da ke karkashin ikon 'yan ta'addan Daesh (ISIS).

Bayanin ya ce wanann dai ba shi ne karon farko da jiragen yakin Amurka suke safke irin wadannan akwatuna, domin kuwa su kan yi kure a wasu lokuta su safke a wurin da ke karkashin sojin sa kai na Iraki, kuma abubuwan da ke ciki makamai ne da suka hada da bindigogi da albarusai da bazuka da dai sauransu.

Wannan taimako na Amurka ga 'yan ta'addan ISIS yana zuwa ne bayan sanar da fara farmakin tsarkake yankin yammacin Mausul daga 'yan ta'addan na wahabiyyah takfiriyya na ISIS.