Sojojin Iraki Na Ci Gaba Da Samun Nasara A Mosul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18068-sojojin_iraki_na_ci_gaba_da_samun_nasara_a_mosul
Rundinar sojin Iraki na ci gaba da samun nasara a yakin da take na neman kwato yankin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 27, 2017 05:51 UTC
  • Sojojin Iraki Na Ci Gaba Da Samun Nasara A  Mosul

Rundinar sojin Iraki na ci gaba da samun nasara a yakin da take na neman kwato yankin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh.

Ko a jiya Lahadi  rundunar ta sanar da sake kwato yankin Mamoun dake a yammacin birnin na Mosul.

A Sanarwar da ta fitar, rundunar da ke yaki da 'yan ta'adda ta kasar ta ce ta shiga yankin na Mamoun ne wanda ke kuriyar kudu a yammacin birnin Mosul a ranar 24 ga wata,

Rundunar da ke yaki da 'yan ta'addan Iraki ta samu nasarar 'yantar da yankin Mamoun baki daya bayan wani kazamin fada da 'yan IS.

A ranar 19 ga watan nan da muke ciki ne, firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi, ya sanar da kaddamar da matakin soja na sake kwato yammacin birnin Mosul.