Kim Jong-Un Ya Bada Umurnin Korar Jakadan Malaysia
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya bada umurnin korar jakadan Malaysia a kasarsa.
A baya bayan nan dai dangantaka na kara yin tsami tsakanin kasashen biyu tun bayan da Malaysia ta fa bincike akan kisan dan uwan shugaban Koriyar ta Arewar da aka kashe a fikin jirgin saman Kuala Lampur.
Koriya ta arewa dai na cewa akwai son rai a binciken da hukumomin Malaysian keyi kan kisan Kim Jon Nam wanda dan uwan shugaban Koriya ta Arewar ne Kim Jon Un.
A makon daya gabata ne Malaysia ta sanar da korar jakadan Koriya ta Arewa daga kasarta, tare da katse duk wata hulda dake tsakanin kasashen biyu.
Hakan kuma ya biyo bayan da kasar ta Malaysia ta bukaci shugaba Kim Jong-Un ya nemi gafara a gare ta saboka kalamensa na sukan hukumomin kasar akan binciken da suke kan kisan dan uwansa Kim Jong-Nam.