Birtaniya Na Goyan Bayan Samar Da Kasashen Palestinu Da Isra'ila
Ministan harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson, ya ce gwamnatin kasarsa na goyan bayan samar da kasashen Palestinu da Isra'ila, wanda hakan ne kawai mafita ta samar da zamen lafiya a yankin.
Mista Johnson na bayyana hakan ne ga manema labarai a yayin da ya isa birnin Ramallah bayan ya gana da takwaransa na Palestinu Riyad al-Malki.
Wannan ziyara ta Mista Johnson ta zo a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin Donald Trump na Amurka ta haifar da koma baya akan duk wani yunkurin kasa da kasa na shawo kan rikicin da aka shafe shekaru da dama anayi tsakanin Palestinu da Isra'ila.
A yau Laraba ne ministan harkokin wajen na Birtaniya ya isa yankin gabas ta tsakiya inda ya gana da shugaban Palestinawa Mahmoud Abbas a Ramallah, kana ya kuma gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Biritaniya dai na daga cikin kasashe mambobin kwamitin tsaro na MDD da suka amunce da kudirin takawa mahukuntan yahudawan sahayoniya birki akan ci gaba da mamayar filayen al'ummar Palestinu.