Syria : Mutane 60 Suka Mutu A Jerin Hare-haren Damascos
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18444-syria_mutane_60_suka_mutu_a_jerin_hare_haren_damascos
Rahotanni daga Syria na cewa a kalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Damascos.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 12, 2017 02:20 UTC
  • Syria : Mutane 60 Suka Mutu A Jerin Hare-haren Damascos

Rahotanni daga Syria na cewa a kalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu a jerin hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Damascos.

Har kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai wadanan hare-hare, saidai tuni aka fara dangantasu dana kungiyar nan da akafi sani da Da'esh.

Galibin dai wadanda suka rasa rayukansu alhazai ne mabiya shi'a 'yan asalin kasar Iraki.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a Damascos babban birnin kasar ta Syria a cikin shekaru shida na yakin basasa da kasar ke fama da shi.

Tunda farko dai wasu alkaluma da hukumar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasa a Syria (OSDH) ta fitar sun ce akalla mutane 59 ne suka ras arayukansu da suka hada da 'yan shi'a 47 da kuma wasu jami'an tsaro Syria 12 da kuma wasu da dama da suka raunana ciki har da masu munanen raunuka.