Kungiyar Fateh al-Sham Ta Dauki Alhakin Kai Harin Damascus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18462-kungiyar_fateh_al_sham_ta_dauki_alhakin_kai_harin_damascus
Kungiyar Fateh al-sham wace ta kasance tsohon reshen Al'Qaida a kasar Syria ta ce ita ce keda alhakain kai munanen hare haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Damascus na kasar Syria.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Mar 12, 2017 12:26 UTC
  • Kungiyar Fateh al-Sham Ta Dauki Alhakin Kai Harin Damascus

Kungiyar Fateh al-sham wace ta kasance tsohon reshen Al'Qaida a kasar Syria ta ce ita ce keda alhakain kai munanen hare haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Damascus na kasar Syria.

Kamfanin dilancin labaren faransa na AFP ya rawaito wata sanarwa da kungiyar mai da'awar jihadi da na cewa wasu gwarzayenta biyu ne suka kai harin na jiya Asabar.

Kawo yanzu mutane 74 ne aka tabbatar da mutuwarsu a jerin hare haren da aka kai kan mabiya mazahbar shi'a galibi 'yan asalin kasar Iraki dake ziyara a wani tsohon gari dake Damascus.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a Damascus babban birnin kasar ta Syria a cikin shekaru shida na yakin basasa da kasar ke fama da shi.

Tun da farko dai wasu alkaluma da hukumar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta kasa a Syria (OSDH) ta fitar sun ce akalla mutane 59 ne suka ras arayukansu da suka hada da 'yan shi'a 47 da kuma wasu jami'an tsaro Syria 12 da kuma wasu da dama da suka raunana ciki har da masu munanen raunuka.