An Zargi Kasashen Turkiyya Da Qatar Da Ruruta Wutan Ayyukan Ta'addanci
Wani dan Majalisar Dokokin Kasar Masar ya zargi kasashen Turkiyya da Qatar da hannu a ruruta wutan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya tare da bayyana su a matsayin maha'inta.
A zantarwarsa da kafar watsa labaran Far na kasar Iran a yau Litinin: Ali Sawah dan Majalisar Dokokin Kasar Masar ya furta cewa: Kasashen Turkiyya da Qatar suke karfafa ayyukan ta'addanci a kasashen yankin gabas ta tsakiya, sakamakon haka ya zame dole a kan kasashen yankin su dauki matakan dakile wannan makirci.
Ali Sawah ya kara da cewa: A fili yake kasashen Turkiyya da Qatar gami da Saudiyya suke daukan nauyin ayyukan ta'addanci da ake gudanarwa a kasashen Iraki, Siriya da kuma Libiya, don haka akwai bukatar samun hadin kai tsakanin kasashen yankin da nufin wargaza wannan makirci da maha'intan kasashe suke kitsawa da nufin cimma wasu munanan manufofinsu na siyasa.