An dakile kokarin kawar da Gwamnatin Siriya
Jaridar Alkabas ta kasar Kuweit ta bayyana duk wani kokari da kawar da halartacciyar Gwamnatin Siriya da rashin cin nasara
A yayin da take ishara kan kasawar kasashen Yamma na samar da Gwamnatin amshin shatan su a kasar Siriya, Jaridar Alkabas ta Kuweit ta bayyana cewa Kokarin Kasashen Yamma na kawar da Gwamnatin Al'ummar Damuscus wacce ta yi fice wajen yaki da Gwamnatin HKI ya ci tira. yayin da take suka kan ci gaba da jayayya gami da yaki domin kawar da halartacciyar Gwamnatin Bashar Al-Asad na Siriya, Alkabas ta rubuta cewa,Lokacin ya yi da za a kawo karshen zubar da jini a kasashen Siriya, Libiya da kuma Yemen, kuma kamata ya yi Kungiyar kasashen hadin kan kasashen Larabawa ta dauki mataki na kawo karshen wannan al'amari.
Alkabas ta kara da cewa kasashen Yamma suna raunana Dakarun tsaron kasashen Laraba a kasashen Masar, Siriya, Iraki bisa da'awar yaki da ta'addanci.kuma kasashen Amurka da kawayenta na kokarin rufe ta'addancin da Haramcecciyar kasar Isr'ila ke yi a yankin zirin Gaza na Palastinu, amma daga karshe ba su nasara ba ganin yadda Al'ummar kasashen suka tashi domin kalubalantar wannan al'amari.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Siriya ta fada cikin rikici, bayan da wasu kasashen Larabawa bisa goyon bayan Amurka suka dinga kwaso 'yan ta'adda daga kasashen Duniya suna shigar da su cikin kasar ta hanayar kasar Turkiya da nufin kifar da Gwamnatin Bashar Al'asad.