Rasha Za Ta Horada Mayakan Kurdawa Syria
Dakarun Kuradwa na Syria zasu samu wani horon kan aikin soja daga kasar Rasha a wata yarjejeniya da bangarorin biyu suka cimma, kamar yadda kungiyar Kurdawa ta sanar a yau Litini.
Wannan dai ita ce yarjejeniya irin ta farko tsakanin mayakan Kurdawa na Syria da kasar Rasha dake marawa gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad baya akan yaki da 'yan tawaye da kungoyoyin masu ikirari da sunan Jihadi.
kakakin kungiyar Kurdawan mai suna (YPG), Redur Xelil ya shaidawa kanfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa zasu samu horo na dabarun fada na zamani.
Kuma a cewarsa zasu fara samun horon nan bada dadewa ba a sansanin Afrine dake yankin Halep, inda tuni sojojin Rasha suka iasa a yankin.
A cen baya dai Amurka ce dai ke talafawa mayakan kurdawan a yakin da ake da 'yan ta'adda na (IS)
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin Rasha ta fara dasawa da kasar Turkiyya wace ke kyallon mayakan Kurdawan a matsayin makiya da take dangantawa da 'yan ta'adda