Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ya Isa Kasar Iraki.
Da safiyar yau alhamis babban sakataren majalisar dinkin duniya antonio guterres isa kasar Iraki.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; manufar ziyararsa a kasar Iraki, ita ce gani da ido akan halin da 'yan gudun hijira su ke ciki.
Antonio Guterres ya kuma jaddada cewa; kare rayukan fararen hula yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci a cikin kowane irin yanayi.
A jiya laraba da ya gabatar da jawabi a taron kasashen larabawa a kasar Jordan, ya tabo batun fararen hula a yaki da wajabcin basu kariya da mafaka, haka nan kuma taimakawa 'yan gudun hijira.
Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh, ta fara kai hare-harenta ne a cikin kasar Iraki, a 2014 tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu kasashen larabawa da su ka hada da Saudiyya.