Syria : Makami Mai Guba Ya Kashe Mutum 58
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19108-syria_makami_mai_guba_ya_kashe_mutum_58
Kungiyar da ke sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a Syria, ta ce, an kai wani hari da makami mai guba a garin Khan Sheikhun da ke karkashin ikon 'yan tawaye.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 04, 2017 06:24 UTC
  • hoto: AFP
    hoto: AFP

Kungiyar da ke sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a Syria, ta ce, an kai wani hari da makami mai guba a garin Khan Sheikhun da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Harin dai na wannan safiyar a cewar Kungiyar ta OSDH ya yi sanadin mutuwar mutane 58.

galibin wadanda harin ya ritsa dasu fararen hula ne da suka hada da yara 11. 

Kungiyar ta  ce galibin mutanen sun mutu ne sanadin shakar wani iskar gas mai guba, saidai kawo yanzu bata kai ga bayyana irin nau'in gas din ba.

rahoton ya ce da akwai fararen hula da dama da yanzu haka suke fama da matsalar numfashi.