Martanin Syria Kan Zarginta Da Yin Amfani Da Sanadarai Masu Guba
Gwamnatin kasar Syria ta mayar da martani dangane da batun kai hari da makami mai guba a yankin Idlib.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta habarta cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Miqdad ya dora alhakin mutuwar fararen hula sakamakon shakar isgar gas mai guba a kan 'yan ta'adda da suka jibge wadannan makamai a Idlib, da kuma gwamnatocin da ke mara musu baya, musamman ma gwamnatocin Birtaniya, Faransa, Da Turkiya gami da Saudiyya, wadanda ya ce su ne suka mika ma 'yan ta'addan sanadarin sarrin mai guba.
Miqdad ya ce wane irin alfanu ne gwamnatin Syria za ta samu idan ta jefa makamai masu guba a kan fararen hula? ya ce wadanda za su amfana da hakan a siyasance yanzu haka suna gudanar da taruka a Brussels da majalisar dinkin duniya, domin samun damar matsa lamba kan gwamnatin Syria.
Ya kara da cewa a cikin 'yan makonnin da suka gabata, gwamnatin Syria ta bayar da bayanai ga hukumar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya, a kan cewa 'yan ta'addan Nusra Front sun shigo da sanadarai masu guba a cikin kasar Syria, amma babu wata gwamnati daga cikin gwamnatocin turai da ta ce uffan kan hakan.