An Dage Tattaunawar Siriya Zuwa 13 Ga Wata
Mar 06, 2016 02:55 UTC
An dage tattaunawar neman zamen lafiya a Siriya zuwa ranar 13 ga watan nan na Maris.
kamar yadda mai shiga tsakanin a rikicin kasar Mr Stiffan Di Mistura ya sanar a wannan Asabar, ya ce bayan tattaunawa da bangarorin da rikicin ya shafa an dage tattaunawar har zuwa 13 ga wata.
A hannu daya kuma Mr Di-Mustura ya nuna fargabar sa akan yarjejeniyar tsagaita wuta dake tangal-tangal a kasar ta Siriya.
tun da farko dai a ranar 9 ga watan nan ne aka shirya zamen tattaunawar a Geneva tare da halartar wakilan gwamnatin Siriya da kuma na 'yan adawa da zumar samun mafita a rikicin kasar da aka shafe sama da shekara hudu ana yi.
Tags