Fara Tattaunawa Tsakanin Wakilin MDD Da Tawagar Gwamnatin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i196-fara_tattaunawa_tsakanin_wakilin_mdd_da_tawagar_gwamnatin_siriya
An Fara Tattaunawa Tsakanin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musaman da wakilan gwamnatin Siriya A Birnin Ganeva.
(last modified 2018-08-22T06:57:45+00:00 )
Feb 02, 2016 13:29 UTC
  • Fara Tattaunawa Tsakanin Wakilin MDD Da Tawagar Gwamnatin Siriya

An Fara Tattaunawa Tsakanin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musaman da wakilan gwamnatin Siriya A Birnin Ganeva.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musaman Staffan de Mistura ya fara tattauwa tare da tawagar gwamnatin kasar Siriya kalkashin jagorancin Bashar Ja'afari a birnin Janeva, a wannan tattaunawar Mista Mistura zai bayyanawa tawagar gwamnatin ta Siriya yadda tattaunawarsu ta gudana da bangaren 'yan adawa a jiya Litinin.

Ana sa ran tattaunawar sulhun na Siriya dake gudana a birnin Gaveva zai fi maida hankali kan batun da ya shafi na jin kai.

Bayan ganawarsu da wakilin MDD, mai magana da yawun 'yan adawar Siriya mista Salim Musalad ya gabatar da jawabi a gaban manema labarai jiya, inda ya ce a halin yanzu tawagarsu na jiran sakamakon da wakilan Majalisar za su basu bayan sun tattaunawa da wakilan gwamnatin Siriya.

Ana sa ran, wakilan Majalisar Dinkin Duniyar za su sake ganawa da bangaren 'yan adawa bayan sun tattauna da tawagar wakilan gwamnatin Siriyan A yau.