Syria Na Shirye Don Tsagaita Wuta A Khan Cheikhoun
Ministan tsaron Rasha ya sanar da cewa dakarun kasar Syria a shirye suke domin tsagaita wuta a Khan Cheikhoun domin baiwa kwararu na kasa da kasa damar shiga yankin don aiwatar da bincike kan zargin amfani da iskar gas mai guba.
A ranar ga watan Afrilun nan ne kasashen dake goyan bayan 'yan tawayen Syria suka zargi gwamnatin Syria da amfani da iskar gas mai guba a yankin na Khan Cheikhoun dake kudancin Iblid ba tare da ma anyi binkice ba.
Mutane kimanin 100 ne galibi yara suka rasa rayukansu a harin yayin da wasu 400 suka raunana.
A makon daya gabata dai kasashen Iran da Rasha sun bukaci hukumar dake hana yaduwar makamai masu guba ta Duniya (OIAC) data kafa wata sabuwar tawaga da zata gudanar da binkice akan ko anyi amfani da makaman masu guba da kuma ko ta ya ya aka isa dasu a yankin da lamarin ya auku.
A halin da ake ciki dai ma'aikatar harkokin kudi ta Amurka, ta bayar da sanarwa sanya takunkumi ga ma'aikata 271 na gwamnatin kasar Syria, masu nasaba da shirin kirkirar makaman kare dangi na gwamnatin kasar.