Syria : Dakarun Kurdawa 28 Suka Hallaka A Hare-haren Turkiyya
Apr 26, 2017 11:06 UTC
Hukumar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta kasa a Syria ta ce adadin mutanen suka rasa rayukansu a hare-haren da jiragen saman Turkiyya kan dakarun Kurdawa ya kai 28, kana wasu 19 na daban suka raunana.
Tunda farko dai rundinar kurdawan ta (YPG) ta ce dakarunta 20 ne suka mutu a hare-haren ciki har da wata kwamanda a cewar kakakin rundinar Abdel Rahmane.
Wannan dai shi ne hari irinsa mafi muni da Turkiyya ta kai kan kurdawa a wannan kasa ta Syria.
Turkiyya dai na kare kanta da cewa kungiyar kurdawan mai alaka da kungiyar PKK da cewa babbar barazana ce gare ta tana kuma danganta ta da kungiyar ta'addanci.
Tags