Na'im Kassim: Fursunonin Palasdinawa Su Ne Sautin Gwagwarmaya
(last modified Fri, 05 May 2017 06:28:27 GMT )
May 05, 2017 06:28 UTC
  • Na'im Kassim: Fursunonin Palasdinawa Su Ne Sautin Gwagwarmaya

Mataimakin Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Ya ce; Fursunonin na Palasdinawa suna ci gaba da gwagwarmaya ne akan 'yan sahayoniya ta hanyar jaruntar da su ke nunawa.

Mataimakin Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah Ya ce; Fursunonin na Palasdinawa suna ci gaba da gwagwarmaya ne akan 'yan sahayoniya ta hanyar jaruntar da su ke nunawa.

Sheik Na'im Kassim ya kuma kara da cewa; Gwagwarmayar da fursunonin na Palasdinawa su ke yi  na tona asirin shugabannin kasashen larabawa ne da su ke kawance da 'yan sahayoniya, su ka kuma zabi kaucewa daga goyon bayan adalci da gaskiya.

Tun a ranar 17 ga watan Aprilu ne dai fursunonin na Palasdinawa da su ke cikin gidajen kurkuku, su ka fara yajin cin abinci saboda siyasar nuna wariya da su ke fuskanta daga 'yan sahayoniyar.

A halin da ake ciki da akwai palasdinawa 500 tsare a gidajen kurkukun Isra'ila da su ka kunshi mata 62 da kananan yara 300.

Al'ummar Palasdinu dai suna nuna goyon bayansu ga fursunonin nasu.