Syria : An Fara Aiwatar Da Yarjejeniyar Kafa Tuddan Mun Tsira
Bayanai daga Syria na cewa an samu dan sukuni a yankunan dake fama da rikice-rikice, bayan fara aiwatar da yarjejeniyar kafa tuddan mun tsira a kasar.
Kasashen Rasha, Iran da Turkiyya ne suka cimma yarjejeniyar a ranar Alhanis data gabata a birnin Astana na kasar Kazakstan da nufin samar da wasu yankunan da zasu zamen tuddan mun tsira ga fararen hula domin rage zubar da jini.
A wannan Asabar ce da misalin karfe 12 na dare ogogon wurin wato 9 agogo na GMT aka tsara yarjejeniyar za ta fara aiki a cewar mataimakin ministan tsaro kasar Rasha Alexandre Fomine, amman tun kafin hakan an samu ragowar rikice-rikice sai dai dan abunda ba a rasa ba.
A ranar 4 ga watan Yuni mai zuwa ne ake sa ran yarjejeniyar zata fara aiki gadan-gadan bayan kasashen da suka cimma yarjejeniyar sun shata yankunan hudu da dokar za ta shafa har tsawan watanni shida.
Ana tsammanin cewa, kafa yankunan zai taimakawa bangarorin dake rikici a Syria, tsagaita bude wuta da fara shawarwarin shimfida zaman lafiya a lokacin da ya dace.