Damuwar MDD Kan Karuwan 'Yan Gudun Hijrar Iraki
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda 'yan gudun hijrar garin Mausil na Kasar Iraki ke karuwa.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Stephen Dojarik kakakin Saktare Janar na MDD a jiya Litinin na cewa Mutanan dake zaune a yankunan dake kalkashin kungiyar IS na gabashin birnin Mausil suna bukatar taimakon gaggauwa.
Tun daga shekarar 2014 Kungiyar ta'addanci ta ISIS ta mamaye wasu yankuna na arewa da yammancin kasar Iraki, a watan Janairun da ya gabata ne Sojoji da Dakarun sa kai na kasar Iraki suka tsarkakke gabashin Mausil baki daya daga mamayar 'yan ta'addar ISIS.
A halin da ake ciki, Sojojin da Dakarun sa kai na kasar Irakin na yakar 'yan ta'adda ISIS a yammacin garin Mausil inda yanzu haka suka 'yanto sama da rabi na yankin yammacin garin na Mausil.