Hamas Ta Jaddada Gwagwarmayar 'Yantar Da Palasdinu
Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta fitar da sanarwar cewa: Kungiyar zata ci gaba da gwagwarmaya da makami har sai ta kai ga kwato hakkokinta daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
A bayanin da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta fitar a yau Litinin a lokacin zaman taron tunawa da cikan shekaru 69 da mamaye yankunan Palasdinawa: Kugiyar ta Hamas ta jaddada cewa hanyar gwagwarmaya da makami ne kawai zai kai al'ummar Palasdinu ga dukkanin hakkokinsu da yahudawan sahayoniyya suka kwace tsawon shekaru.
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Babu wata nasara da al'ummar Palasdinu suka samu a tsawon shekarun da suka kwashe suna tattaunawa da nufin kai wa ga hakkokinsu daga yahudawan sahayoniyya, don haka abin da karfi ya kwata, karfi ne kawai zai kwato shi.
Ranar 14 ga watan Mayun wannan shekara ce aka cika shekaru 69 da kwace yankunan Palasdinawa, inda yahudawan sahayoniyya suka aiwatar da kashe-kashen gilla kan al'ummar Palasdinu tare da mamaye musu kasa.