Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kai Harin Kan Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20480-sojojin_gwamnatin_haramtacciyar_kasar_isra'ila_sun_kai_harin_kan_palasdinawa
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan Palasdinawa a garin Nablus da ke gabar yammacin Kogin Jordan.
(last modified 2018-08-22T07:00:07+00:00 )
May 18, 2017 07:42 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kai Harin Kan Palasdinawa

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan Palasdinawa a garin Nablus da ke gabar yammacin Kogin Jordan.

Tawagar motocin yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a yau Alhamis ta kusa cikin yankin Dir-Sharaf da ke yammacin garin Nablus suna harbe-harbe kan gidajen Palasdinawa.

Har ila yau a cikin daren jiya Laraba wayewar garin yau Alhamis sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila sun farma kauyen Yasid da ke arewacin garin na Nablus, inda suka dinga barin wuta kan gidajen na Palasdinawa.

Ya zuwa yanzu babu labarin irin hasarar da hare-haren wuce gona da irin suka janyo.