Siriya : Harin Bom Ya Kashe Mutum Hudu
May 23, 2017 06:47 UTC
Rahotonni daga Syria na cewa wani harin bom da aka kai da mota ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkta wasu talatin na daban a birnin Homs.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan sanarwar da sojojin gwamnatin kasar suka bayar na cewa sun kwace daukacin ikon birnin..
Harin dai an kai shi ne a kusa da unguwar al-Zahra ta galibi musulmi yan Alawuya kabilar da shugaban kasar Bashar Al-Assad ya fito.
Unguwar al-Zahra dai ta jima tana fuskantar ire-iren wandanan hare-haren kuma mafi yawa kungiyar 'yan ta'ddan nan ta IS ce ke daukan al'hakin kaisu.
Tags