Saudiya Ta Koro 'Yan Ghana 5,00
Mahukuntan Saudiyya sun dauki matakin tuso keyar wasu 'yan kasar Ghana su kimanin 5,00 wadanda ke rayuwa a kasar ba bisa ka'ida ba.
A watan Maris daya gabata ne hukumomin Saudiya suka baiwa yan kasar ta Ghana wa'adin kwanaki 90 domin su fice daga kasar.
Mafi akasarin mutanen dai wadanda yan aiki ne a cikin gidaje ko gadi sun fuskanci muzguna da walakanci iri daban daban a kasar ta Saudiyya.
Ofishin jakadancin Ghana a birnin Riyad da kuma karamin ofishin jakadancin Birnin Jeddah sun baiwa mutanen wasu takardu domin tsaukaka masu balaguro don komawa gida.
Offishin jakadancin dai ya ce yana nadamar yadda ake cin zarafin mutanen da hadin kan mutanen Saudiyya ba tare da hukumomin kasar sun ce uffan ba akan batun.