Takun-Saka Tsakanin Qatar Da Saudiyya Na Kara Tsananta
Tun bayan da rikicin da ke tsakanin Saudiyyah da Qatar ya fito fili sakamakon sanar da yanke dukkanin alaka da kasar Saudiyya ta yi da Qatar kwanaki uku da suka gabata, lamurran suna ci gaba da kara dagulewa a tsakanin kasashen larabawan yankin tekun Fasha.
Saudiyya ta bayyana Qatar a matsayin mai daukar nauyin ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda, wadanda suke barazana gare ta da kuma sauran kasashen larabawan yankin, haka nan kuma Qatar tana da kyakkyawar alaka da Iran, sabanin siyasar Saudiyya da wasu daga cikin kasashen yankin tekun Fasha.
Wannan mataki a kan Qatar dai ya shafi kasashe uku ne kawai daga cikin kasashe 6 na yankin tekun Fasha, wato Saudiyya, Bahrain da kuma UAE, yayin da Kuwait da kuma Oman suka ki bin sahun wadannan kasashe uku a kan wannan mataki da suka dauka a kan Qatar, inda suke kokarin ganin sun sulhunta tsakanin sauran kasashen da kuma Qatar, duk kuwa da cewa ga dukkanin alamu babu wani ci gaba da aka samu ta wanann fuska, bayan da sarkin Kuwait ya ziyarci Saudiyya a jiya a kan wannan batu, ya kuma koma gida a tsakar daren jiya Talata ba tare da bayyana wani ci gaba da aka samu a kan wannan batu ba, amma ministan harkokin wajen Saudiyya Adel Jubair da yake ziyara a birnin paris na Faransa ya bayyana a yammacin jiya cewa, Saudiyyah za ta iya shiryawa da Qatar ne kawai idan ta daina taimaka ma kungiyoyin Hamas da Muslim Brotherhood, wadanda ya kira kungiyoyin 'yan ta'adda.
Sai dai baya ga Saudiyya wasu daga cikin kasashen larabawa daga wajen yankin tekun Fasha da suke dasawa da Saudiyya da suka hada da Masar, Libya da kuma Mauritania, sun shelanta yanke duk wata alaka da kasar ta Qatar, domin mara baya ga matakin na Saudiyya.
Duk da cewa an jima ana takun saka tsakanin Qatar da Saudiyya a kan batutuwa daban-daban, amma dai lamarin ya fito fili ne tun daga lokacin ziyarar Donald Trump a Saudiyyah, inda Saudiyya ta bayyana ma Trump cewa Qatar ce ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci, kamar yadda Trump din da kansa ya bayyana cewa lallai Saudiyya ta tsegwanta masa hakan.
Da dama daga cikin masana harkokin siyasa ta duniya sun yi imanin cewa, batun kyakkyawar alaka ta diflomasiyya tsakanin Qatar da Iran ba shi ne dalilan daukar wannan mataki a kan Qatar ba, domin kuwa alakar da ke tsakanin kasashen Oman da Iran tafi alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, haka nan kuma alakar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin Iran da UAE, tafi karfin alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, amma Saudiyya ba ta dauki irin wannan mataki a kansu ba.
Dangane da batun daukar nauyin kungiyoyin ta'addanci kuwa, kowa ya sani cewa Saudiyyah ce ta kafa kungiyar alkaida, kuma ta kafa ISIS wadda reshe ne na Alkaida a Iraki, daga bisani kuma ta zama kungiyar ta'addanci mafi girma da bunkasa a duniya, da ma wasu kungiyoyin da ta kafa daga bisani a Syria masu dauke da irin wannan akida, to amma kuma Qatar ta yi wa Saudiyya shigar sauri, inda ta kulla alaka da dukkanin wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda masu da'awar jihadi da sunan addini ko sunnah da Saudiyya ta kafa, har ma Qatar ta zama tafi Saudiyya kusanci da su saboda irin kudaden da take kashe musu, da ba su makamai domin kai hare-hare a cikin Syria da nufin kifar da gwamnatin shugaba Assad.
Irin wannan aiki ne Qatar ta yi ma Saudiyya a Libya, inda a halin yanzu Qatar tafi Saudiyya karfin fada a ji a wurin kungiyoyin 'yan ta'adda a Libya, haka lamarin yake a kasar Yemen, inda Saudiyya tare da UAE suke iko da birnin Aden, to amma daga bisani UAE ta yi wa Saudiyyah juyin mulki, inda mayakan da take marawa baya suka kwace iko da wurare masu muhimamnci a birnin danga hannun masu biyayya ga Hadi Mansur wanda Saudiyya ke marawa baya, yayin da ita kuma Qatar take yaki da su baki daya ta hanyar yin amfani da mayakan alkaida da ISIS da suke a cikin Yemen, haka lamarin yake a majalisar larabawan tekun fasha, Qatar ba ta yin biyayya ga umarnin Saudiyya kamar yadda kasashen UAE da Bahrain suke bin Saudiyya ido rufe, maimakon haka ma a wasu lokuta ta kan kalubalanci Saudiyya, sabanin Kuwait da Oman wadanda suna bin Saudiyya amma ba ido rufe ba, amma kuma ba su kalubalantar ta kamar yadda Qatar ke yi, wanda hakan yasa Saudiyya take kallon kasar Qatar ta zame mata tamkar wata kishiya a cikin lamurranta a yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran harkoki da suka shafi kasashen larabawa.
Baya ga haka kuma batun harin 11 ga watan Satumba 2001, wanda dukkanin kungiyoyin leken asiri na Amurka suka tabbatar da cewa jami'an Saudiyya ne suke da hannu a cikin lamarin, a kan haka Amurkawa sun taso Saudiyya a gaba a kan wannan batu, duk kuwa da irin kariyar da Barack Obama ya yi ta baiwa Saudiyya a lokacin mulkinsa, a kan haka ya zama dole a kan Saudiyya ta sama ma kanta mafita, musamman ganin cewa a lokacin da Donald Trump yake yakin neman zabe ya sha alwashin cewa matukar dai ya lashe zabe, to kuwa tabbas zai shiga kafar wando daya da Saudiyya a kan kafa kungiyoyin 'yan ta'adda da take yi da kuma daukar nauyinsu, wannan ne ya sanya Saudiyya ta yi amfani da makudan kudade na fitar hankali domin rufe bakin Donald Trump da sauran Amurkawa masu sukar ta a kan batun ta'addanci, wanda hakan ne ya sanya Amurka ta janye sunan Saudiyya daga cikin masu daukar nauyin ta'addanci, tare da nuna wa duniya cewa a halin yanzu ma Amurka za ta kafa kawance na yaki da ta'addanci tare da Saudiyya da wasu kasahe da aka tattara shugabanninsu a birnin Riyadh a lokacin ziyarar Trump makonni biyu da suka gabata, wato tamkar Saudiyya ta zama ita ce mai yaki da ta'addanci a halin yanzu.
Saudiyya ta yi amfani da wannan dama, inda ta dora laifin kaco kaf a kan kasar Qatar, duk kuwa da cewa Saudiyya da Qatar laifinsu iri daya ne, shi ne daukar nauyin ayyukan 'yan ta'adda, a nan Saudiyya ta samu damar jifar tsuntsu biyu da dutse guda, na daya ta samu kariya daga tuhumar mara baya ga kungiyoyin 'yan ta'adda, na biyu kuma a daya bangaren ta huce haushinta a kan Qatar.