Saudiyyah Ta Hana 'Yan Qatar Shiga Harami Domin Yin Umrah
Sakamakon yanke alakar da Saudiyya tare da wasu kasashen da gwamnatin Qatar, mahukuntan saudiyya sun hana wasu 'yan kasar Qatar gudanar da aikin Umrah.
Jaridar Al-sharq ta kasar Qatar ta bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na kasar Qatar Ali bin Sumaikh Al-marriya bayyana cewa, 'yan kasar Qatar da ke zaune a Saudiyya da kuma wadanda suka je aikin Umrah suna fuskantar cin zarafi daga mahukuntan saudiyyah, inda ake hana su shiga cikin masallacin haramin Makka domin gudanar da ibada.
Jami'in ya ce kwamitinsa ya samu korafi irin wannan ya kai kimanin 700 a cikin kasa da kwanaki 5 da suka gabata.
Saudiyya da da wasu kasashen larabawa da take dasawa da su da kuma wasu kasashen da take baiwa taimakon kudade a Afirka, sun sanar da yanke alaka da Qatar saboda zarginta da taimaka wasu kungiyoyi da suka kira na 'yan ta'adda, da suka hada da Hamas da kuma kungiyar 'yan uwa musulmi mai mazauni a kasar Masar.