Afganistan : An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Wani Masallacin Kabul
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane hudu ne suka rasa rayukan kana wasu takwas na daban suka raunana sakamakon wani harin kunar bakin wake a wani masallacin 'yan Shi'a dake birnin Kabul.
Hukumomin kasar sun ce maharan sun tayar da bam din su ne a wurin dafa abinci na masallacin, bayan da 'yan sanda suka hana su shiga cikin masallacin.
Kakakin ma'aikatar cikin gidan kasar Najib Danish, ya bayyana a shafinsa na tweeter cewa fararen hula uku ne da wani dan sanda guda suka rasa rayukansu a yayin harin na ta'addanci da aka kai a masallacin Al-Zahra dake yammacin Kabul.
An dai kai harin ne a yayinda masu ibadar ke shirin tarurukan (Laylat al-Qadr) wanda keda matukar mahimmanci wajen 'yan shi'a kasancewarsa daren zagayowar ranar shahadar Iman Ali (AS).
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin, a yayin da kungiyar taliban ta yi tir da harin tana mai nisanta kan ta da kai hare-hare a wuraren ibada.