Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Masu Yawa A Kasar Pakistan
Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da ofishin babban jami'in rundunar 'yan sandan garin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan.
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Pakistan Shahzada Farhat ya sanar da cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da ofishin babban jami'in rundunar 'yan sandan garin Quetta fadar mulkin lardin Baluchistan da ke shiyar kudu maso yammacin kasar Pakistan a safiyar yau Juma'a lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 11 tare da jikkatan wasu fiye da 20 na daban kuma halin wasu daga ciki ya munana.
Ya zuwa yanzu baba wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, kuma babau wani mutum da aka kama da hannu a shirya kai harin, duk da cewa: garin Quetta yana daga cikin jerin garuruwan lardin Baluchistan na kasar Pakistan da suka fi fama da matsalolin tashe-tashen musamman fuskantar hare-haren kungiyoyin 'yan ta'adda masu kafirta musulmi.