Mutane 57 Suka Mutu A Harin Pakistan
Hukumomi a Pakistan sun ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai jiya a wata kasuwar yankin Parachinar ya kai 57.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu a harin da akwai wasu sama da 200 da suka raunana a cewar sanarwar.
An dai kai harin ne a yayin da kasuwar ta cika makil da jama'a a yayin da ake shagulgulan bikin karamar sallah dake kawo karshen watan Azumin Ramadana mai alfarma.
Bayanai daga kasar sun kuma ce an kai wani hari na daban a ranar ta Jumma'a a wani offishin yan sanda na lardin Quetta dake yankin Baloutchistan inda mutane 14 da suka hada da 'yan 10 suka mutu.
Babu dai tabas akan ko wacce kungiya ce ka da alhakin kai harin, kasancewar kungiyoyi da dama masu ikirari da sunan da jihadi ciki har da IS sun ce su keda alhakin kai harin.