Ra'ayul Yaum: Zaman Sirri Tsakanin Larabawa Da Isra'ila A Masar
(last modified Thu, 29 Jun 2017 17:36:23 GMT )
Jun 29, 2017 17:36 UTC
  • Ra'ayul Yaum: Zaman Sirri Tsakanin Larabawa Da Isra'ila A Masar

Jaridar Ra'ayul Yaum ta nakalto daga wata majiyar diplomasiyya ta larabawa da ke tabbatar da cewa an gudanar da zama a tsakanin Isra'ila da wasu larabawa a kasar Masar

Jaridar wadda take watsa labaranta ta hanyar yanar gizo daga birnin London, wadda take mayar da hankali kan siyasar kasashen larabawa da yankin gabas ta tsakiya, ta habarta cewa, majiyoyin diplimasiyyar sun tabbatar mata da cewa an gudanar da zaman ne a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar a makon da ya gabata.

Jaridar ta kara da cewa, an gudanar da wannan zaman a sirri ne a tsakanin wakilan Isra'ila, Saudiyya, Amurka, UAE, Masar da kuma Jordan, kuma zaman yana da dangantaka ne da batun yankin Palastinawa na zirin Gaza, da ke karkashin ikon kungiyar Hamas, wadda dukkanin kasashen da suka halarci zaman suke kallonta a matsayin kungiyar ta'adanci.

Zaman ya gudana ne a cikin sirri matuka, a kan haka babu cikakken bayani kan abubuwan da aka tattauna dalla-dalla, amma bisa ga dukkanin alamu akwai wani boyayyen lamari da ake kitsawa a kan yankin na Gaza, da Isra'ila take ci gaba da killace shi tsawon shekaru.