Iraki : IS Ta Yi Garkuwa Da Mutane 900 A Hawija
Jul 01, 2017 10:03 UTC
Majiyoyi wanda ba na gwamnati ba daga Iraki na cewa kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta yi garkuwa da mutane kimanin 900 a lardin Hawija dake kudu maso yammacin yankin Kirkik.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da hukumomin kasar ta Iraki ke cewa ana gad da murkushe kungiyar ta IS ko kuma Daech a Mosul.
A shekara 2014 ne kungiyar 'yan ta'addan ta mamaye lardin na Hawija bayan data kwace ikon birnin Mosul.
So tarin yawa dai 'yan ta'addan da zarar sun shiga tsaka mai wuya kan yi garkuwa da mutane don kawo cikas a yakin da ake da su.
A halin da ake ciki dai dakarubn kasar ta Iraki na ci gaba da yaki da sauren mayakan kungiyar da suka buya a tsohon birnin Mosul.
Tags