Katar: Ba Mu Tsoron Harin Sojan Saudiyya.
(last modified Sun, 02 Jul 2017 19:14:51 GMT )
Jul 02, 2017 19:14 UTC
  • Katar: Ba Mu Tsoron Harin Sojan Saudiyya.

Ministan harkokin wajen kasar Katar ya ce; kasarsa ba ta da tsoron duk wani harin da Saudiyya za ta kai wa kasarsa

Ministan harkokin wajen kasar Katar ya ce; kasarsa ba ta da tsoron duk wani harin da Saudiyya za ta kai wa kasarsa.

Muhammad Bin Abdurrahman ali Thani wanda cibiyar Le Formiche ta kasar Italiya ta yi hira da shi, ya fada a yau lahadi a birnin Rom cewa; Bukatun da kasashen da su ka killace Katar su ka gabatar, sun ci karo da hankali, kuma abinda Saudiyyar ta ke so, ya sabawa 'yanci da cin gashin kan kasar Katar.

Muhammad Bin Abdurrahman ya ce; Katar ba ta ganin kimar bukatu 13 na kasashen Saudiyya, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain.

Daga cikin bukatun kasashen da akwai rufe gidan telbijin din aljazeera, da  rufe tashar sansanin sojan kasar Turkiya a Doha, sai kuma rage alakar diplomasiyya da Iran.