Katar : Bayanin Saudiyya Da Kawayenta Ya Sabawa Dokokin Kasa Da Kasa
(last modified Sat, 08 Jul 2017 06:50:30 GMT )
Jul 08, 2017 06:50 UTC
  • Katar : Bayanin Saudiyya Da Kawayenta Ya Sabawa Dokokin Kasa Da Kasa

A jiya jumaa ma'aikatar harkokin wajen kasar Katar ta sake watsi da bayanin da kasar Saudiyya da kawayenta su ka fitar, tare da cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa.

A jiya jumaa ma'aikatar harkokin wajen kasar Katar ta sake watsi da bayanin da kasar Saudiyya da kawayenta su ka fitar, tare da cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kasashen Saudiyya, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar sun fitar da bayanin hadin gwiwa a jiya juma'a da a ciki su ka zargi Katar da kokarin hargitsa zaman lafiya a yankin tekun pasha.

Kasashen hudu sun yanke alakar jakadanci da kasar ta Kasar tare da yin kira gare ta da ta rufe tashar telbijin din aljazeera da rage huldar diplomasiyya da Iran. Haka nan kuma sun zargi Katar din da taimakawa ta'addanci da kudade.

Katar ta yi watsi da bukatun na Saudiyya da kawayenta.