Iraki: An Halaka Jasim Abu Hafsa Daga Cikin Manyan Kwamandojin ISIS
Rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da halaka daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ISIS Jasim Abu Hafsa Al-Saudi dan kasar Saudiyya.
Majiyar dakarun kasar ta Iraki ta tabbatar wa manema labarai cewa, a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da 'yan ta'addan ISIs suke tserewa daga Mosul , wasu daga cikinsu sun tsallaka koramar Dajlah, wasu kuma an halaka su kafin su tsallaka koramar.
Bayanin ya ce daga bisani an samu gawar Jasim Abu Hafsa Al-saudi dan kasar Saudiyya, wanda yana daga cikin manyan kwamandojin kungiyar kuma daya daga cikin manyan na hannun damar Abubakar Albaghdadi, wanda shi ma yana daga cikin 'yan ta'addan da aka halaka a lokacin da suke hankoron tserewa daga Mosul ta hanyar tsallaka koramar Dajlah, kamar yadda aka nuna hoton gawarsa a kafofin yada labaran kasar Iraki.
A wani labarin kuma Abu Haisam Al-Ubaidi ya nada kansa a matsayin jagoran kungiyar ta 'yan ta'addan wahabiyawa na ISIS, amma wasu daga cikin mayakan kungiyar ba su amince da nadin nasa ba, lamarin da ya jawo harbe-harbe da kashe-kashe a tsakaninsu.